Kundin Tattara Bayanan Mustabsirin (Encyclopedia)
Jan 24 2024
Bugawa Da Yaɗa Mujalladi Na Farko Na Littafin (Mausu’ar) Mustabsirin
Littafin (Mausu’ar) Mustabsirin
Cikin luɗufi na Ubangiji da inaya ta Ahlul Bait Ma’asumai (a.s) tare da tsayuwar-daka da himmar kwamitin ilimi na Cibiyar Mustabsirin wannan littafin (Mau’su’ar) Mustabsirin an kammala buga shi da yaɗa shi.
An fara yaɗa mujalladi na farko na littafin (Mau’su’ar) Mustabsirin daidai da ranakun tunawa da Shahadar Sayyida Fatima Azzahra (s).
Mujallar Mustabsirin
May 4 2024
Ladar Sanar da Al’umma Makarantar Ahalulbait a Mahangar Mirza Shirazi
Ladar Sanar da Al’umma Makarantar Ahalulbait a Mahangar Mirza Shirazi
Ƙoƙari da ƙwazon shekaru 15 sun yi sanadin canja ƙauyen ‘yan Sunna zuwa Shi’a
Ayatullah Wahid Khurasani (Allah ya ƙara tsawon kwana):
A zamanin Mirza Shirazi wani ɗalibi ya zo ƙofar gidansa yana sanye da tsofaffin kaya ya ce: “Ina son ganin Mirza… Mutane suka ce masa: Mirzan da ba shi da lokacin hatta mujtahidai, sai kai ka wani zo ka ce kana son ganin sa?!
Mar 30 2024
RAYA DAREN 19 GA RAMADAN, LAILATUL KADARI NA FARKO
A ranar Juma’a 18 ga watan Ramadan 1445 bayan Hijira dalibai mazauna unguwar Shaharake Mahadiyye wadanda suka hada daga ‘yan kasashe daban-daban na Afrika da kuma ‘yan kasashe irin su Pakistan da Indiya da Indunisiya da Siriya da sauransu suka gudanar da munasabar raya daren lailatul Kadari domin neman tabarruki da neman kusanci zuwa ga Allah da neman gafara da budi da yalwar arziki da daukaka ga Musulunci da Musulmai a duk fadin duniya.
Bayan karatun Qur’ani da addu’oi an kuma gabatar da jawabi a wajen zaman wanda ya gudana a Masallacin Bilal da ke unguwar ta dalibai ta Shaharake Mahadiyye, Qum, Iran.
Wannan wasu kadan ne daga cikin hotunan da aka dauka a wajen taron:
Mar 30 2024
DAREN DA AKA SARI AMIRUL MUMINA ALI (a.s)
DAREN DA AKA SARI AMIRUL MUMINA ALI (a.s)
19 Ramadan shekara ta 40 bayan Hijira
Tarihin faruwar wannan abin yana da tsawo, to amma bisa la’akari da lokaci da kuma saƙon da ake son a isar a wannan taƙaitaccen rubutun a kuma dare irin wannan na 19 ga watan Ramadan, sai mu ce:
Bayan yarjejeniyar yaudara da aka yi a yaƙin Siffin abin da ake kira Tahkim tsakanin Amr bn Aas da Abu Musa Ash’ari, to wasu ƙungiyoyi daga cikin Musulmi sun fanɗare wa Amirul Muminina Ali (a.s) wanda ake kiransu Khawarijawa, duk da cewa Amirul Muminin ɗin ya yi ta ƙoƙarin nusantar da su kan wannan tafarki da suka ɗauka da kuma ba su lokaci ko sa tuba, amma dai sun ƙi yin hakan sai ma dai suka dinga tara sojoji don yaƙar sa da kuma halasta jininsa, abin da ya haifar da yaƙi a tsakaninsu, yaƙin da ake kira da Yaƙin Nahrawan.More
Mar 25 2024
Haihuwar Imam Hasan Mujtaba (a.s)
An haifi Imam Hasan al-Mujtaba (a.s) ne ranar sha biyar ga watan Ramalana mai albarka shekara ta uku bayan hijira. Mahaifansa kuwa su ne tsarkakan halittun nan guda biyu wato: Imam Ali da Kuma Fatima al-Zahra (a.s). Haihuwarsa ke dawuya sai aka sanar da Manzon Allah al-Mustafa (s.a.w.a) da kuma albishir saboda wannan karuwa da aka yi, shi kuma sai ya garzaya gidan Fatima (a.s) don taya murna da farin nuna farin cikinsa.
Koda isowarsa sai aka gabatar masa da wannan jariri mai albarka, Manzo ya karbe shi da hannayensa mai daraja, ya sumbace shi, ya rungume shi a kirjin sa; sai ya kira sallah a kunnensa na dama, ya yi ikama a na hagu, don sautin gaskiya ya zama farkon sautin da ya fara ratsa samuwarsa da jinsa. Sai Manzo (s.a.w.a) ya juyo ya kalli Ali (a.s) ya ce: “Wane suna ka sa ma dan nawa?” Sai Imam Ali (a.s) ya ce: “Ban kasance mai shiga gabanka ba.” sai Manzo ya ce: “Kamar yadda ni ma ban kasance mai shiga gaban Ubangijina ba.” (Wato ma’ana ni ma ba zan gabaci Ubangiji wajen sa masa suna ba. Wannan tataunawa ba ta kai gacinta ba sai ga Wahayin Allah na sauko wa ga Manzon Allah (s.a.w.a), wanda ke sanar da shi cewa Allah Madaukaki Ya sanyawa abin haihuwa suna Al-Hassan.
Mar 18 2024
Shi’anci Shi ne Musulunci na Haƙiƙa ba na Zahiri ba
Bismillah wa Billah
Shi’anci Shi ne Musulunci na Haƙiƙa ba na Zahiri ba
Tambaya: Shin Shi’anci Shi ne Musulunci na Haƙiƙa?
Eh, gaskiya ina son in zama ɗan Shi’a, sai dai wata mas’ala ‘yar ƙarama tana ruɗar da ni, kuma har yanzu na kasa samar mata mafita. A saboda haka nake neman in samu wani ɗan Shi’ar da zai taimaka min in sami warwarar wannan mas’alar ko na samu natsuwa, kammalalliyar natsuwar da za ta ba ni damar da zan iya yin riƙo da mazahabar Ahalilbait (a.s).
Domin gaskiya idan abin in zama Shi’a ne, to zan sami kaina ina mai fuskantar abubuwa guda biyu; kuma dole ne in zaɓi ɗaya a cikin biyun:
Mar 18 2024
RAMADAN KARIM – ALLAH YA BA MU ALBARKARSA
Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah
RAMADAN KARIM
Muna taya daukacin masu bibiyar wannan shafin na Cibiyar Duniya ta Mustabsirin murnar shigowar wannan wata na Ramadana mai albarka da alfarma.
Watan albarka, watan Ibada, watan yawaita karatun Kur’ani da yawaita addu’a da ambaton Allah su Hailala da Tasbihi da Tahmidi da Istigfari da Uwa-uba yawaita Salatin Annabi (s.a.w). Haka nan ma wata ne na ciyarwa wato ciyar da raunana masu karamin karfi mabukata wadanda a yankunanmu ga su nan birjik ba iyaka, marayu ne a’a matan da mazajensu suka mutu ne ko suka sake su da dai sauran mabukata masu yawa.
Mar 11 2024
Mene ne maudu’in Littafin: ‘Mu’utamaru Ulama’il Bagdad’?
Mene ne maudu’in Littafin: ‘Mu’utamaru Ulama’il Bagdad’?
Littafi: Mu’utamaru Ulama’il Bagdad
‘Mu’utamaru Ulama’il Bagdad’ wato Mu’utamar ɗin Malaman Bagdad: Sunan littafi ne ta’alifin Maƙatil bn Aɗiya al-Bakari a nasaba, kuma Ba-hanafe a mazhaba, sirikin Nizam Malik al-Ɗusi; ɗaya ne daga cikin malaman ƙarni na biyar. A cikin littafin yana naƙalto munazara wato tattaunawa ta ilimi wacce ta gudana a tsakanin Husain bn Ali Al-Alawi malamin Shi’a da kuma Abbasi shugaban malaman Ahalissunna na wancan lokacin, an gudanar a tsawon kwana 3 a birini Bagdad, wanda hakan ya kai ga Sarki ya Shi’ance da waziri da mafi yawan malamai da ministoci da sauran mahalarta zaman. Daga baya aka buga littafin aka yaɗa shi a karon farko a shekarar 1958 a birnin Karachi.
Mar 11 2024
Margit ‘yar ƙasar Jamus ta yi Istibsari
Mustabsira Margit a Ziyararta ga Haramin Imam Ali (a.s)
Margit mustabira ta ƙasar Jamus ta samu ziyartar makwancin Imam Ali (a.s) a Haraminsa da ke Najaf mai tsarki.
A yayin da ake tattaunawa da ita a Cibiyar Duniya mustabira daga ƙasar Jamus ta bayyana cewa: Halayen Musulmin da muka yi zama da su a ƙasata ya mini tasiri kuma ya janyo hankalina baki ɗayansa; har sai da na kai ga na samu yaƙini a kan cewa lallai Musulunci yana kare wa mace mutuncinta da ƙimarta da darajarta.
Mar 11 2024
Taron Ashura Ne Ya Shi’antar Da Ni (Juzibi Bunu (Yusuf))
Taron Ashura Ya Mini Tasiri Har Ya Zama Sanadin Musuluntata…Juzibi Bunu
Na kasance Kirista kuma an haife ni a Birtaniya, a saboda haka sam ban san komai a kan ilimin Musulunci da mazahabar Shi’a ba. Na kasance ina da abokai Musulmai, sai dai sam ba ma su kula da addinin ba ne, addinini ba ya gabansu.
Mar 9 2024
Wasiƙar wani Mustabsir Malam Hassam
Assalamu alaikum wa Rahmatullah wa Barakatuh. Ni da ɗan uwana bayan mun ga lamarin Da’ish (ƙungiyar nan mai kafirta sauran Musulmi da yaƙarsu da kashe su ba bisa haƙƙi ba) a gidajen talabishin; wannan sai ya sa kawai muka tsunduma bincike a kan Musuluncin ɓangaren Sunnarsa da Shi’arsa. To a cikin binciken namu sai muka fahimci cewa lallai Sunnanci musamman aƙidar (Wahabiyanci da Salafanci) maƙwadaitan shuwagabanni da masu son mulki ne suka samar da su, kuma lallai aƙida ce mai tayar da zaune tsaye mai wuce gona da iri. Sannan sai muka yi bincike a kan akidar Shi’a sai muka samu cewa aƙida ce da take a kan gwadabe wanda yake tsaka-tsaki kuma babu ƙetare iyaka babu tayar da zaune tsaye a ciki. Kuma wannan babu shakka shi ne Musuluncin da Allah da Manzonsa (s.a.w) suke so.
Mukabalolin Mustabsirin
Mar 17 2024
Muƙabalar Da Ta Wakana Tsakanin Dakta Isam Imad Da Shek Usman Kamis
Muƙabalar Da Ta Wakana Tsakanin Dakta Isam Imad Da Shek Usman Kamis
Muƙabala Ta Farko:
Shek Mustafa Ɗa’i (Alƙalin Zama)
Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai; Muƙabala ta farko wadda za a yi ta wannan ofis ɗin da ake kira da (Gurfatul Haƙ) wato ofis ɗin Shi’a Isna Ashariyya.
Sayyid Rafiƙ Musawi kuma shi ne shugaba mai jagorantar zaman daga ɓangaren Shi’a Isna Ashariyya, sai ya ce:
Jan 23 2024
Muhawarar Mustabsir Ibrahim Kulibali Tare Da Ɗaya Daga Cikin Malaman Sufaye
Muhawarar Mustabsir Ibrahim Kulibali Tare Da Ɗaya Daga Cikin Malaman Sufaye
Ibrahin Kulibali
Karo a Cikin Karo
Kulibali yana ba da labari game da wani abu da ya faru yana mai faɗin cewa: “Mafi yawan rayuwata na yi ta ne a hannun gwaggota; kuma ta kasance tana tsananin ƙaunata har ta kai ga tana ji da ni fiye da ‘ya’yanta, kuma tana burin ina ma dai a ce in zama babban malamin addini in na girma, a saboda haka ne ma take ta ƙarfafani a kan hakan, to kuma dama gwaggon tawa Basufiya ce ‘yar Ɗariƙar Tijjaniya.
Kafar Yadawa
Mar 19 2024
Saƙo Daga Sayyid Basil Khadra’ – Mustabsir ɗan ƙasar Falasɗinu
Saƙo daga mustabsir ɗan ƙasar Falasɗinu samahatul Sayyid Basil Khadra’, a yayin wani shiri na soshiyal midiya (social media).
Ga saƙon nasa kamar haka:
An ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Misalin Ahlilbait ɗina a cikinku kamar kwatankwacin jirgin Nuhu ne, duk wanda ya hau jirgin ya tsira wanda kuma ya ƙi hawa to ya halaka zuwa wuta. Kuma lallai (Annabi) Nuhu (a.s) ya ce wa ɗansa: Ya ɗan ɗana! Zo ka hau tare da mu mana, kada fa ka kasance tare da kafirai!
Labaran Masu Istibsari
May 5 2024
Yaya Aka Yi Na Zama Ɗan Shi’a? In Ji (Malam Jahri Singapore)
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai
Yaya Aka Yi Na Zama Ɗan Shi’a? In Ji (Malam Jahri Singapore)
Malam Jahri (Ɗaya Daga Cikin Tsofaffin Manyan Wahabiyawa a Ƙasar Singapore) Ya Yi Magana Game Da Yadda Ya Fahimci Shi’anci.
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai
Na gode wa Allah da ya shiryar da ni zuwa ga hanya madaidaiciya, hanyar nan kuwa ita ce cikakkiyar koyarwar addinin Musulunci bisa haskakawar Imamai goma sha biyu na Shi’a.
May 4 2024
Ba’amerikiya Matar Wani Musulmi Ta Musulunta
Ba’amerikiya Matar Wani Musulmi Ta Musulunta
Wata mata Ba’amerikiya wacce ta canja addininta zuwa Musulunci, ta ba da labarin yadda ta fahimci Musuluncin.
Shekaru masu yawa kafin ta Musulunta ta auri wani Musulmi, sai dai wannan auren bai sanya ta Musulunta ba. Ita da mijinta sun yi wa junansu alƙawarin za su yi zama na kawar da kai game da aƙidun juna kuma kowannen su zai yi addinin da yake so ba tare da tilastawa ba.
May 3 2024
Tarihin Musuluntar Roch Boulvin, Likita ɗan ƙasar Belgium, (Tsohon) Shugaban Sashen Tiyata a Asibitin Imam Rida (a.s) Mashhad
Tarihin Musuluntar Roch Boulvin, Likita ɗan ƙasar Belgium, (Tsohon) Shugaban Sashen Tiyata a Asibitin Imam Rida (a.s) Mashhad
Tsawon lokaci, mutane ‘yan ƙasa sun sha zuwa Hubbaren Khaje Rabi domin ziyartar waɗanda suka rigaye mu gidan gaskiya, amma sai suka dinga lura da wani rubutu a jikin ƙabarin farfesa Boulvin, sai dai ba su san waye wannan mutumin da ke kwance a wannan ƙabarin kuma mai ya yi a rayuwarsa ba.
A wannan rubutun muna son mu yi bayani a taƙaice game da rayuwar wannan jajirtaccen gwarzon likitan da kuma tarihin Musuluntarsa.
Apr 29 2024
Luigi (Ammar) De Martino Ya Musulunta
Luigi (Ammar) De Martino ya Musulunta
An haifi Luigi (Ammar) De Martino a Italiya a shekarar 1937, a lokacin da yake saurayi ya kasance fasto ne a cocin evangelical. Amma yadda ‘yan evangelical ɗin suke goyon bayan tsarin rayuwar Amurkawa ya sanya ya ja baya daga gare su.
Apr 17 2024
Mustabsira ‘Kamila Salsatinu’ Brazil
‘Kamila Salsatinu’
Mai Matar nan ‘yar ƙasar Brazil ɗin ta Musulunta ta faɗa ne a kan hijabi?
‘Kamila Salsatinu’ matar da ta Musulunta ‘yar ƙasar Brazil, ɗaya ce daga cikin mutanen da Allah ya tsamo ta daga cikin duhun jahilci da gafala ta dace da faɗinsa Subhanahu wa Ta’ala: “Allah shi ne masoyin waɗanda suka yi imani, yana fitar da su daga duffai zuwa haske”, a lokaci guda kuma ta yi riƙo da koyarwar Sayyida Fatima Azzahara (s) wajen kiyaye hijabi. A cikin wannan tattaunawa da ita za mu ga bayaninta a kan yadda ta fahimci tafarkin shiriya wato Musulunci da kuma riƙonta da hijabi.
Mai Tambaya: Shin malama Kamila kafin ki Musulunta wane addini kike yi?
Mar 19 2024
BABBAN MUSTABSIRI NA NAHIYAR AFRIKA – SHEK IBRAHIM ZAKZAKI (H)
SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H)
TAKAITACCEN TARIHIN SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H)
An haifi Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), a unguwar Kwarbai da ke cikin garin Zaria ta jihar Kaduna a ranar 15 ga Sha’aban 1372 Hijiriyya (Miladiyya: 28 April, 1953).
Mahaifinsa shi ne Malam Yaqoub, dan Malam Ali, dan Sharif Tajuddeen, dan Liman Husaini, wanda asalinsu tsatson Manzon Allah Muhammad (S) ne, ta hanyar Imam Hasanul Mujtaba (AS), wanda suka iso kasar Hausa daga garin Shingidi da ke tsohuwar daular Mali ta da.
KARATUN ALKUR’ANI DA LITTATTAFAI A ZAURUKAN MALAMAN ZAZZAU
Bayan tasowar Shaikh Zakzaky, ya yi karatun littattafan addini a wajen Malamai daban-daban a garin Zazzau. Ya fara da karatun Alkur’ani a wajen mahaifinsa, da kuma karatun wani littafin Fiqihun Malikiyya mai suna ‘Jiddil Aaziz’ a wajen kakarsa Haajar (da ake kiranta Maikaratu).
Ya kuma cigaba da karatun Alkur’ani (na Allo) a gidan Sarkin Ladanan Zauzzau na lokacin, da kuma wajen Malam Sani Abdulkadir, wanda shi bayan karatun Alkur’ani ya rika hada musu da littafan Fiqihun Malikiyya da kuma Larabci. Banda karatun bai-daya, Shaikh Zakzaky ya rika saka littattafai a gaban Malam Sani Abdulkadir, inda ya sauke littafai irinsu Akhdari, Ishmawi, ‘Dan-Rushdi, ‘Dan-Ashir, Qurdabi, Badamasi, ‘Ya Dalibal Li’irabi, Mulha, Ajruma, Rubu’iyya da sauransu, wadanda duk littafan Fiqihu ne da na Lugga a kasar Hausa a wancan lokacin.
Mar 16 2024
Bukar bn Bukar – Mustabsir ɗan ƙasar Murtaniya
Bukar bn Bukar – Mustabsir ɗan ƙasar Murtaniya
An haife shi a shekarar 1379H daidai da 1960M a birnin Butilimit a ƙasar Murtaniya, kuma ya taso a cikin gidan da ba na mabiya Ahlulbaiti (a.s) ba. Sai dai sannu a hankali ya fara tasirantuwa da mazahabar Shi’a har dai daga ƙarshe ya gamsu da wannan mazahaba har ya shelantar shigarsa ciki a shekarar 1427H daidai da 2007M a birnin Nu’akchot a ƙasar Murtaniya. Sannan sai ya fara yaɗa wannan fikira ta Shi’anci ta hanyar yin tabligi domin isar da wannan saƙo na makarantar Ahlulbaiti (a.s) ga dukkan al’ummar Murtaniya.
SHI’A A ƘASAR MURTANIYA
Mar 12 2024
Ali ɗan jarida mutumin ƙasar Jordan
Shi’ancewar Ali ɗan jarida mutumin ƙasar Jordan
Birnin Jordan
Ali ya ce: Yana da cikakkiyar masaniya a kan matsin da zai fuskanta bayan ya zama Shi’a. Ya ce: Na yi ƙaura daga fahimtar da nake a kai zuwa fahimtar da ta fi waccan tsarki da dalilai. Na rubuta wasu littafai kuma na san madamar aka buga su a Jordan, to abin zai shafi rayuwata da aikina kai zan ma fuskanci barazana da rashin tsaro daga mutanen unguwa.
Wallafe-wallafen Mustabsirin
Jan 22 2024
A Albarkacin Hasken (Sayyida) Fatima Na Shiriya
A Albarkacin Hasken (Sayyida) Fatima Na Shiriya
Sunan Littafi: A Albarkacin Hasken (Sayyida) Fatima Na Shiriya
Marubuci: Abulmun’im Hasan Sudani
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai; wannan littafi labari ne mai ratsa zuciya na wani masanin shari’a mutumin Sudan game da yadda ya fahimci mazahabin Ja’afariyya (Shi’a Imamiyya)
Feb 3 2024
LITTAFIN: ALBID’ATU WAL IBTIDA’U
ALBID’ATU WAL IBTIDA’U; Ta’alifin Abdulhamid Al-Jaf.
Silsilatul Kitabi Wassunnati (Halƙa Ta Uku).
Halƙa Ta Uku
Wannan Littafi A Halƙarsa Ta Uku Ya Ƙunshi: Sujjada A Kan Turba Da Bayyana Bisimillah (A Cikin Salla) Da Haɗa Salloli Da Shafa a Kan Ƙafa Da Ɗora Hannu A Kafaɗa Da Sakin Hannu Da Taƙiyya Da Mutu’a.
Dukkan waɗannan bahasosin an yi su a cikin wannan littafin tare da kawo hujjoji da dalilai daga Alƙur’ani da Sunna Sharifiyya.
Littafin an rubuta shi da harshen Larabci, muna ƙoƙarin tarjama shi zuwa harshen Hausa ba da jimawa ba insha Allah.
Mar 13 2024
Hankali a Rayuwar Dan’adam / Dr. Ammar Al-Makki
A cikin wannan shiri mutum zai karu da bayani game da wasu ka’idodi na bahasin Hankali. Shi ko hankali kamar yadda muka sani a gaskiyar magana shi ne mutum saboda ba a komai da marar hankali a rayuwar nan, kai ba a ma lissafa marar shi a matsayin mutum. To kuma a lokaci guda ma’abocin hankalin shi ma yana bukatar ya saita hankalin nasa bisa ka’idodi….Wanda a nan za a ji wasu daga ciki.
Mar 14 2024
ZAGIN SAHABBAI BA MUSULUNCI BA NE1 / MALAM BELLO DANKOLI
Har kullum bayanan da Shi’a suke yi shi ne: Tabbas ba sa zagin sahabbai, domin zagi a Musulunci haramun ne, aya ta fada mana cewa: Kada ku zagi wadanda suke kiran wanin Allah…. Wato Mushirikai da kafirai. To idan zagin su Allah ya hana, ina ga zagin Musulmai kuma Musulman ma sahabbai wadanda suka taimaki Annabi wajen isar da wannan sako na Musulunci.
To amma inda gizon ke saka shi ne: Shi’a suna karanta abubuwan da suka faru a zamanin sahabbai na rigingimu da sakin hanyar da wasu suka yi da kin bin umarnin Annabi na wasici da ya yi masu a Gadir Khum da dai sauran matsaloli. Sai dai mu sani ba fa wai dukkan sahabbai ne suka aikata ba a’a tarihi bai bar mu a duhu ba, ya zayyano mana wadanda suka yi din. Mutum ya je ya bincika zai gani. Fadin hakan kuma ba zagi ba ne sam.
Tarihin Rayuwar Mustabsirin
Jan 30 2024
Shahid Shek Hasan Shahata (Allah Ya Ɗaukaka Shahadarsa)
Shahid Shek Hasan Shahata (Allah Ya Ɗaukaka Shahadarsa)
An haife shi a shekara ta 1365H daidai da 1964M a ƙauyen Harbiɗ a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Abu Kabir ta Gundumar Al-Sharƙiyya Masar, ya tashi a gidan addini ‘yan mazahabar Hanafiya.
Bisa la’akari da gidansu gida ne na ma’abota addini sai ya zama ya fara karatunsa na Ƙur’ani tun daga ƙuruciyarsa; haka nan kuma mahaifinsa ya tarbiyantar da shi a kan son Ahlul Baiti (a.s).
Hasan yana ba da labari dangane da yarintarsa yana cewa: Na taso tun ina yaro ƙarami da son Ahlul Baiti (a.s) da biyayyarsu. Domin mahaifina ya tarbiyyartar da ni da dukkan ‘yan gidanmu a kan sonsu; sau da yawa yana ba ni labari game da matsayin Imam Ali (a.s), yakan ce min: Ya ɗana!
Jan 21 2024
Shugaban Malaman Ahlul Sunna Na Faransa Ya Shi’ance
shek Sanko Muhammadi
Na Kasance a Some Cikakkiyar Suma; Da na Fahimci Shi’anci Sai na Farfaɗo
Sayyid Walid Al-Ba’aj ya ce: shek Sanko Muhammadi limamin masallaci da cibiyar Ifta’i a lokaci guda kuma shugaban malaman Ahlul-sunnah na Faransa ya shelanta Shi’ancewarsa a birnin Karbala mai tsarki a lokacin da yake ziyartar ƙasar Iraƙi.
Sayyid Al-Ba’aj ya ƙara da cewa: Tabbas an san shek Sanko Muhammadi wurin ayyukansa na gina masallatai, kodayake asalinsa mutumin Kamaru ne amma yana zaune a Faransa sama da shekaru 43, har ma ya mallaki takardar shedar dan ƙasa (Faransa). Sayyid Ba’aj yake cewa a karonsa na farko na ziyartar Iraƙi da ziyartarsa Karbala na haɗu da shi muka gaisa muka ɗan tattauna a farfajiyar wurare masu tsarki na Karbala a lokacin taron bikin tunawa na (Dausayin Shahada ta Takwas) a inda ɗan uwa mai girma kuma ma’abocin bincike-bincike na ilimi mutumin Tunusiya wato shek Muhammad Saleh Al-Hanshir ya dinga yi mana tafinta (fassara) tsakaninmu kasantuwar yana jin harshen Faransanci da Larabci.
Jan 20 2024
Abdulbaƙi Al-Jaza’iri
Abdulbaƙi Al-Jaza’iri
An haifi Abdulbaƙi a garin Burj Bu-Aririj na ƙasar Aljeriya a shekara ta 1376 Hijriyya wanda ya yi daidai da shekara ta 1957 Miladiyya.
Ya ƙarasa karatunsa a jami’ar Faransa a inda ya samu takardar shedar Masters degree a sashen Education (ilimin tarbiyya da koyarwa).
Dakta Abdulbaƙi Al-jaza’iri ya fahimci Shi’anci ne a shekara ta 1407 Hijriyya, wato shekara ta 1987 Miladiyya a ƙasar Siriya, a inda ya gamsu cewa mazahabar Ahlul-Bait (a.s) ita ce a kan gaskiya. Ya zauna zuwa wani ɗan lokaci ya ci gaba da zama a Siriyar, sannan daga baya ya kama hanya zuwa ƙasar Iran, wanda kuma har zuwa yau yana zaune ne a ƙasar.
Jan 18 2024
Tijjani Samawi
Sayyid Muhammad Tijjani Samawi
Dakta Sayyid Muhammad Tijjani Samawi (mutumin da ya shahara da Tijjani Samawi) ɗan asalin ƙasar Tunusiya. An haife shi a shekara ta 1936 Miladiyya, kuma ya fito a cikin babban gida ma’abota addini a garin Ƙaudah da ke kudancin ƙasar ta Tunusiya.
A nan garin nasu (Ƙaudah) ya yi karatunsa na firamare da sakandare, sannan daga nan kuma sai ya wuce wata kwaleji ta ilimi da sana’a ya ɗora karatunsa, a inda ya samu takardar shedar zama injiniya (muhandis). Tun yana yaro matashi yake da matuƙar son karance-karancen ilimomin addini kuma kasantuwar yana da ƙwazo da himma sai ya zama ya haɗa ilimi da taƙawa, a saboda haka ne ma sai ya zama tun da wannan ƙuruciyar yake limancin salla a masallacin garinsu kuma yake yin tafsirin Ƙur’ani da ba da karatun littafan fiƙihu.
Ya kasance yana mai yawan tafiye-tafiye zuwa ƙasashe irin su Masar da Hijaz (Saudiyya) da Iraƙi da sauransu domin neman ilimi da sani da kuma sauke faralin Hajji da Umara.
Bugawar Cibiya
Jan 24 2024
Bugawa Da Yaɗa Mujalladi Na Farko Na Littafin (Mausu’ar) Mustabsirin
Littafin (Mausu’ar) Mustabsirin
Cikin luɗufi na Ubangiji da inaya ta Ahlul Bait Ma’asumai (a.s) tare da tsayuwar-daka da himmar kwamitin ilimi na Cibiyar Mustabsirin wannan littafin (Mau’su’ar) Mustabsirin an kammala buga shi da yaɗa shi.
An fara yaɗa mujalladi na farko na littafin (Mau’su’ar) Mustabsirin daidai da ranakun tunawa da Shahadar Sayyida Fatima Azzahra (s).
Jan 22 2024
Littafin: Aƙidar Tauhidi a Makarantar Ahlulbait (a.s)
Littafi Mai Daraja Da Aka Rubuta Game Da (Aƙidar Tauhidi a Makarantar Ahlulbait (a.s))
A kwanakin Idin Gadir mai girma da albarka, Cibiyar Mustabsirin ta himmantu da buga tare da yaɗa littafi mai ɗimbin daraja mai suna: (Aƙidar Tauhidi a Makarantar Ahlulbait (a.s)) wato Aƙidar Tauhidi a bisa koyarwar makaranta ta tunani da fikira ta Ahlulbait (a.s), mawallafin littafin shi ne Dakta Ahmad Rasim Al-Nafis mustabsir kuma mutumin Masar.
Wane ne Ahmad Rasim Al-Nafis
– Sayyid Ahmad Rasim Al-Nafis Ma’abocin Himma a Musulunci (Islamic Activist).
– Dan Shi’a Imamiyya.
Dakin Karatu
Mar 21 2024
Fadlul Shi’ati Alal Ummati Fi Hifzil Ƙur’ani Wal-inayati Bihi – Ustaz Marwan Kalifat
Cikin godiya ga Allah fitowar wannan littafi ta kammalu:
Fadlul Shi’ati Alal Ummati Fi Hifzil Ƙur’ani Wal-inayati Bihi
(فضل الشيعة على الأمة في حفظ القرآن والعناية به)
Falalar Shi’a a kan (Sauran) Al’umma
Falalar Shi’a a kan Al’umma a wajen kiyaye Ƙur’ani da kulawa da shi da Shakkala shi da yi masa nuƙuɗa-nuƙuɗa da Tafsirinsa.
Wallafar: Ustaz Marwan Kalifat
Wani yanki na muƙaddimar littafin: Wahabiyawa da waɗanda suka tasirantu da koyarwarsu suna aibata Shi’a kuma suna yawan tuhumar su a kan su kawo ingantaccen sanadi na Ƙur’ani. Yana da ban mamaki lamarin tuhumar nan tasu! Domin wanda gidansa ya kasance na gilas ne, ba zai jefi gidajen mutane da dutsi ba, kamar yadda yake a karin-magana. A saboda haka shin su ɗin sun mallaki ingantaccen sanadin, ballantana a yi maganar tawaturinsa ga ƙira’ar Hafs wacce mafi agalabin Musulmai suke karantawa a yau?!
Mar 13 2024
Husain (a.s): Tsakanin Haihuwa da Shahada Cikin Ruwayar Zahabi da Haisami
Sunan Littafi: Husain (a.s) A Tsakanin Haihuwa Da Shahada Cikin Ruwayar Zahabi Da Haisami.
Sunan Littafi na Asali: (Al-Husain Alaihil Salam Bainal Wiladati Wal Shahadati Fi Ruwayatil Zahabi Wal Haisami).
Mawallafin Littafi: Shek Nazar Aali Sanbul Al-Ƙaɗifi.
A Dunƙule Littafin ya ƙunshi:
Feb 18 2024
Wahada a tsakanin Muwahhidin
Kira zuwa ga Wahada!
Kira ne na Alƙur’ani wanda ayoyi sukutum Allah (swt) ya saukar domin haɗin kai a tsakanin muwahhidin wato masu addinin saukakke daga Allah (swt) wanda ya ƙunshi dukkan abubuwan da ake buƙata na haɗin kai (saboda yadda haɗin kan yake da matuƙar muhimmanci da kuma fa’idar da ke cikin yin hakan).
Feb 5 2024
Littafi: Ayatul Taɗhir
Littafi: Ayatul Taɗhir
Mawallafi: Muhammad Mahadi Asifi
Bugawar: Majma’ul Alami Li Ahlil Bait (a.s)
Sura: Ahzab; Aya ta 33: Bismillahir rahmanir rahim: Innama yuridullahu li yuzhiba ankumur rijsa Ahlal Baiti wa yuɗahhirakum Taɗhira.
Mawallafin littafin ya yi ƙoƙari sosai wajen kawo hujjoji daga Sunna da Shi’a game da fayyace cewa shin wai su wa ake nufi a wannan aya mai girma, haka nan ya kawo lawazim ɗin da ke tattare da ayar kama daga batun Isma da Tsarki da Tsarkaka daga dukkan datti ko saɓo da sauransu da kuma hukunce-hukunce na shari’a da aka iya fitarwa daga ciki.
Feb 3 2024
LITTAFIN: IMAMA DA WILAYA A ALƘUR’ANI
Littafi ne da wasu adadi na malamai suka wallafa a kan Imamancin Ahlul Baiti (a.s) a Alƙur’ani mai girma da hadisai sharifai.
A cikin littafin sun kawo dalilai masu tarin yawa daga Alƙur’ani mai girma da Sunna Sharifiya domin tabbatar da jagorancin Ahlul Baiti (a.s) cewa lallai Manzon Allah (s.a.w) ya naɗa wa al’ummar Musulmi waɗanda za su jagorance su a bayansa kuma ya shelanta masu cewa madamar suka yi ri ƙo da su to ba za su taɓa ɓata ba a bayansa har sai sun same shi a tafkin Kausara.
Daga cikin ruwayoyin akwai inda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa: “Lallai ni mai bari a cikinku ne Nauyaya guda biyu (Saƙalain); (ko Abubuwa masu Daraja da Ƙima guda biyu; (Siƙlain): madamar kuka yi riƙo da su to ba za ku taɓa ɓata ba har abada, kuma lallai su ba za su taɓa rabuwa ba har sai sun iske ni a tabki (tabkin Kausara)).
Jan 5 2024
TAUHIDIN MUFADDAL
KASHI NA FARKO
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI
TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA ANNABI MUHAMMADU DA IYALAN GIDANSA TSARKAKA
GABATARWAR MAI YADAWA
Imaman Ahlul Baiti (a.s) sun kasance suna ƙosar da al’ummah da iliminsu, suna amsa tambayoyin masu tambaya, suna bude ƙofofin sani ga masu nema.
Haƙiƙa Imam Jafar dan Muhammad Al-Sadiƙ (as) yana daga cikin wannan bishiyar mai tsawo da faɗi, kuma bishiyar da tushenta ya tabbata kuma ya kafu a cikin ƙasa, ya yi amfani da wata dama ta raunin daular Umaiyawa, da kuma lokacin da Abbasiyawa suke ƙoƙarin assasa daularsu, saboda haka sai ya assasa babbar makarantarsa ta tunani (hankali), sai daliban ilimi da haƙiƙa suka tuttuɗo gare shi suna kwasar ilimi daga tushensa, More
Apr 6 2024
Shiga Cikin Ƙunci Da Tsananin Rayuwa Ya Zama Sanadin Shiriyata
Shiga Cikin Ƙunci Da Tsananin Rayuwa Ya Zama Sanadin Shiriyata
Bayan bincike mai zurfi da nacewa kan yin addu’oi, na tsinci kaina ina mai miƙa wilayata ga Imam Ali (a.s) a matsayinsa na hasken Musulunci, kuma magajin Manzon Musulunci na haƙiƙa, wanda Allah ne da kansa ya zaɓe shi, ya wajabta mana ƙaunarsa da yin biyayya gare shi.
Ni haifaffiyar ƙasar Czech ce (Jamhuriyyar Czech:) a nan aka haife ni kuma a cocin Katolika aka yi bikin raɗa mini suna domin neman tabarruki, duk da cewa iyayena ba wasu masu kula da addini ba ne can sosai ba, amma dai mun yi imani da Allah sai dai ba ma yin bautar sam-sam. Lokacin da na kai shekara 14 a duniya a lokacin ne na rasa mahaifiyata. Ina ‘yar shekara 18 kuma na yi aure, yanzu haka ina da ɗa a auren da na yi. Amma kasantuwar ƙarancin shekaru, zamantakewar wannan aure sam ba ta yi daɗi ba, zaman aure sam babu fahimtar juna a tsakani.
More
By hs • Kundin Tattara Bayanan Mustabsirin (Encyclopedia) 0