Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci 1446h
Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci: Kamar yadda muka sani a duk ranar daya ga watan Muharram, rana ce da ake lissafinta a matsayin ranar shigowar sabuwar shekarar Musulunci a wajen dukkan Musulmi wato shekarar Hijiriyya Kamariyya, kuma daga nan ne ake fara lissafin wata-wata na watannin Musulunci kama tun daga shi watan na Muharram da Safar […]
Watan Muharram Da Abubuwan Da Ya Kunsa
Watan Muharram wata ne mai alfarma, wata ne da yake daya daga cikin watannin da ake kiran su da Ashhurul Hurum, wato Watanni Madaukaka; wadanda aka haramta yin yaki a cikinsu. Wata ne na farko a kidayar watannin Kamariyya guda goama sha biyu a Musulunci.