Kundin Tattara Bayanan Mustabsirin (Encyclopedia)
Jan 24 2024
Bugawa Da Yaɗa Mujalladi Na Farko Na Littafin (Mausu’ar) Mustabsirin
Littafin (Mausu’ar) Mustabsirin
Cikin luɗufi na Ubangiji da inaya ta Ahlul Bait Ma’asumai (a.s) tare da tsayuwar-daka da himmar kwamitin ilimi na Cibiyar Mustabsirin wannan littafin (Mau’su’ar) Mustabsirin an kammala buga shi da yaɗa shi.
An fara yaɗa mujalladi na farko na littafin (Mau’su’ar) Mustabsirin daidai da ranakun tunawa da Shahadar Sayyida Fatima Azzahra (s).
Mujallar Mustabsirin
Jul 2 2024
Ranar Mubahala
Ranar Da Manzon Allah (S) Ya Fito Yin Mubahala Da Kiristocin Najaran Tana Nufin:
Duk duniya Manzon Allah (saww) ba shi da tamkar waɗanda ya fito da su wato Imam Ali (a.s) da Sayyida Faɗima Azzahara (a.s) da ƴaƴanta Imam Hasan da Imam Husain (a.s) domin da yana da waɗanda suka fi su ko tamkarsu to da ya fito da su a wannan rana. More
Jun 27 2024
Murnar Haihuwar Imam Musa Kazim (a.s)
Wasu Daga Cikin Zantukan Imam Kazim (a.s)
Imamu Kazim (a.s) ya ce: “Mafificin abin da bawa zai kusanci Allah da shi bayan saninsa (sanin Allah) ita ce salla”. Tuhafil Uƙul, sh391.
Imamu Kazim (a.s) ya ce: “Kamar yadda jiki ba ya tashi sai da ruhi rayayye
Jun 26 2024
ALLAH NE YA UMARCI ANNABI MUHAMMAD (S) YA NAƊA ƘANINSA IMAM ALI (AS)
ALLAH NE YA UMARCI ANNABI MUHAMMAD (S) YA NAƊA ƘANINSA IMAM ALI (AS) A MATSAYIN HALIFA NA FARKO A BAYANSA; DA NASSIN AYAR ISAR DA SAKO (AYAR TABLIGI):
Allah (swt) yana cewa:
“Ya kai Annabi (saw)! isar da abinda Allah ya aiko maka; idan ba ka isar ba tamkar ba ka isar da sako ba; tabbas! Allah zai kiyayeka daga mutane” (Q : 5 : 67):
يا ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺑﻠﻎ ﻣﺎ ﺃﻧﺰﻝ ﻣﻦ ﺭﺑﻚ ﻭﺇﻥ ﻟﻢ ﺗﻔﻌﻞ ﻓﻤﺎ ﺑﻠﻐﺖ رسالته
(Al-Ma’ida : 67).
Manyan malaman Ahlus-Sunnah a fagen Tafsiri da Hadisi da Asbabun-Nuzul… Sun tabbatar da cewa wannan ayar ta sauka ne daf da al’amarin Ghadir, kuma bayan Mala’ika Jibril (as) ya sauko da wannan ayar ne Annabi (saw) ya tara Sahabbansa a Ghadir Khum ya shelanta masu cewa Imam Ali (a.s) ne halifa a bayansa:
Fakhrud-Deen Ar-Razi (Babban malamin Ahlus-sunnah) ya tabbatar da cewa; Ayar isar da sako (Ayatut-Tablig) ta sauka ne daf da al’amarin Ghadir, kuma bayan Mala’ika Jibril (as) ya sauko da wannan ayar ne Annabi(saw) ya tara Sahabbansa a Ghadir Khum ya shelanta cewa Imam Ali(as) ne maula (Shugaba / halifa) a bayansa:
Jun 22 2024
TAYA MURNAR HAIHUWAR IMAM ALIYU AL-HADI (AS)
HAIHUWAR IMAM ALIYU AL-HADI (AS)
TAKAITACCEN TARIHIN IMAM ALI AL-HADI(AS):
Nasabarsa ta bangaren mahaifinsa: Imam Ali Al-Hadi (as) ɗan Imam Muhammad Al-Jawad (as), ɗan Imam Ali Ar-Rida (as) ɗan Imam Musa Al-Kazim (as), ɗan Imam Ja’afar As-Sadiq (as) ɗan Imam Muhammad Al’baƙir (as) ɗan Ali Zainul-Abidin (as) ɗan Imam Husain Sayyidus-Shuhada (as) ƙanin Imam Hasan Al-Mujtaba (as) ‘ya’ya Ali bin Abi Talib (as) da Fatimah Az-Zahra (as); ‘yar Annabi Muhammad (S).
Mahaifiyarsa:
Jun 17 2024
Muna Maku barka da Salla – 10 Zulhijja Ranar Salla Babba
Sallar Idin Layya = Babbar Sallah
KA’ABA
*Takaitaccen Tarihin*
*Sayyid Sharif:*
*Shibuli Sharif Ibrahim*
Jun 17 2024
Shahadar Muslim ibn Akil
Shahadar Muslim ibn Akil
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un
A ranar Arfa, Yazidu Ɗan Mu’awuya Jikan Abu Sufiyan da Hindu (Magatsiyar Hantar Syed Hamza) ya sa Hajjaj ya kashe Muslim Ɗan Akeelu, wanda Imam Hussaini(as) ya aike shi garin Ƙufa domin isar da saƙon taimaka masa wurin yaƙar zalunci.
Jun 16 2024
9 Ga Zulhijja Ranar Arfa (1445)
Ranar Arfa
Ranar Arfa wato ranar tara ga watan Zulhijja, ɗaya ce daga cikin ranaku masu matuƙar muhimmanci da ƙima a Musulunci sannan kuma rana ce mai tsarki da aka kwaɗaitar da yin wasu ayyuka na ibada a cikinta saboda girma da matsayi da kuma gafara da rahamar Allah da ta yalwata a wannan yinin.
Jun 14 2024
Tunawa da Shahadar Imam Muhammad Baƙir (a.s)
Shahadar Imam Muhammad Baqir (a.s)
Shi Imam Muhammad Baƙir (a.s) ya fita daban a cikin A’imma (a.s), ta yanda ya zamo shi ta ko ina a nasaba shi:
Muhammady ne kuma Alawi ne sannan Fatimi. Don kuwa Imam Ali ɗan Husain ɗan Ali ɗan Abu Ɗalib (a.s) ne ya haife shi.
Mahaifiyarsa kuwa ita ce Fatima ‘yar Imam Hasan Almujtaba ɗan Ali ɗan Abu Ɗalib (a.s)…
Haka nan shi da ɗansa Imam Ja’afar Assadiƙ (a.s) sun fi duk sauran A’imma samun damar karantar da al’umma koyarwar gidansu, shi ya sa a duniyar Shi’a da Sunna za ku ga Hadisansu sun fi yawa a bisa sauran A’imma (a.s).
Jun 8 2024
Murnar Zagayowar Ranar Auren Haske Biyu (Imam Ali da Sayyida Fatima a.s)
Auren Sayyida Fatima Zahra da Imam Aliyu bn Abi Talib Salamullahi Alaihima.
Allah Ta’ala ya ba Musulunci nasara a yakin Badar a shekara ta 2 bayan hijira. Bayan wata biyu da yaƙin Badar aka daura auren Sayyida Fatima Zahra diyar Annabi Muhammad Mustafa da Imam Ali dan Abu Talib Salamullahi Alaihima.
Jun 7 2024
Juyayin Shahadar Imam Muhammad Al-Jawad (a.s)
Shahadar Imam Muhammad Al-Jawad (A.S)
Wane Ne Imam Muhammad Al-Jawad (a.s) a Takaice
Shi ne Imam Muhammad Jawad (a.s) ɗan Imam Ali Ar-Rida (a.s) ɗan Imam Musa Al-Kazim(as) ɗan Imam Ja’afar As-Sadiƙ (a.s) … In da nasabarsa take tuƙewa zuwa ga Imam Ali (a.s) da Sayyida Fatima (a.s) zuwa ga Manzon Allah (s).
Bayan Shahadar mahaifinsa shi ne ya zama Imami inda ya shekara 17 yana jagorantar al’ummar kakansa Annabi Muhammad (s).
Tarihin Shahadarsa: Ranar 29 ga watan Zulƙi’ida; shekara 220h, daidai da 29 ga November 835m. Ya yi shahadar ne a garin Kazimain.
Dalilin Shahadarsa:
Mukabalolin Mustabsirin
Mar 17 2024
Muƙabalar Da Ta Wakana Tsakanin Dakta Isam Imad Da Shek Usman Kamis
Muƙabalar Da Ta Wakana Tsakanin Dakta Isam Imad Da Shek Usman Kamis
Muƙabala Ta Farko:
Shek Mustafa Ɗa’i (Alƙalin Zama)
Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai; Muƙabala ta farko wadda za a yi ta wannan ofis ɗin da ake kira da (Gurfatul Haƙ) wato ofis ɗin Shi’a Isna Ashariyya.
Sayyid Rafiƙ Musawi kuma shi ne shugaba mai jagorantar zaman daga ɓangaren Shi’a Isna Ashariyya, sai ya ce:
Jan 23 2024
Muhawarar Mustabsir Ibrahim Kulibali Tare Da Ɗaya Daga Cikin Malaman Sufaye
Muhawarar Mustabsir Ibrahim Kulibali Tare Da Ɗaya Daga Cikin Malaman Sufaye
Ibrahin Kulibali
Karo a Cikin Karo
Kulibali yana ba da labari game da wani abu da ya faru yana mai faɗin cewa: “Mafi yawan rayuwata na yi ta ne a hannun gwaggota; kuma ta kasance tana tsananin ƙaunata har ta kai ga tana ji da ni fiye da ‘ya’yanta, kuma tana burin ina ma dai a ce in zama babban malamin addini in na girma, a saboda haka ne ma take ta ƙarfafani a kan hakan, to kuma dama gwaggon tawa Basufiya ce ‘yar Ɗariƙar Tijjaniya.
Kafar Yadawa
Mar 19 2024
Saƙo Daga Sayyid Basil Khadra’ – Mustabsir ɗan ƙasar Falasɗinu
Saƙo daga mustabsir ɗan ƙasar Falasɗinu samahatul Sayyid Basil Khadra’, a yayin wani shiri na soshiyal midiya (social media).
Ga saƙon nasa kamar haka:
An ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Misalin Ahlilbait ɗina a cikinku kamar kwatankwacin jirgin Nuhu ne, duk wanda ya hau jirgin ya tsira wanda kuma ya ƙi hawa to ya halaka zuwa wuta. Kuma lallai (Annabi) Nuhu (a.s) ya ce wa ɗansa: Ya ɗan ɗana! Zo ka hau tare da mu mana, kada fa ka kasance tare da kafirai!
Labaran Masu Istibsari
Jun 22 2024
Addinin Musulunci, A Matsayinsa Na Addini Cikakke… Salim Sa’id Al’rajahi
Malam Salim Sa’id Al’rajahi
Addinin Musulunci, A Matsayinsa Na Addini Cikakke; Ya Umarci Dukkanin Mutane Da Su Nemi Sani Kuma Su Yi Bincike
Malam Salim Sa’id Al’rajahi ya ce: “Addinin Musulunci, a matsayinsa na addini cikakke; ya umarci dukkanin mutane a kan su nemi sani kuma su yi bincike.
Ya ƙara da cewa: Duk wani wanda yake son ya ɗauki matakin da yake daidai, to lallai ne ya
Jun 11 2024
Taƙaitacce Tarihin Malam Junaid Bello Ibrahim Sakkwato
Shek Junaidu Bello Ibrahim
Taƙaitacce Tarihin Malam Junaid Sakkwato
Cikakken suna: Junaidu Bello Ibrahim, ni haifaffen garin Sakkwato ne, amma asalin kakanninmu Nufawa ne da suka taso daga garin Bidda da ke jihar Neja.
An haife ni a 21 ga watan Agusta 1977 a birnin Sakkwato ta Arewa. A nan Sakkwaton na yi karatun makarantar allo har zuwa na yi saukar Al-Ƙur’ani, kamar dai yadda yake a al’adar kasar Hausa Fulani. Sannan kuma na yi karatun firimare (primary) a Salihu Anka Model School, daga nan sai
May 27 2024
Matashiyar Ba’amerikiya: Babban Dalilin Ɗanfaruwata Da Ahalulbait (a.s) Shi Ne Muhadarorin Addini Da Na Sha Saurare Game Da Masifofin Da Suka Fuskanta…
Matashiyar Ba’amerikiya: Babban Dalilin Ɗanfaruwata Da Ahalulbait (a.s) Shi Ne Muhadarorin Addini Da Na Sha Saurare Game Da Masifofin Da Suka Fuskanta…
Mustabsirar Ba-amerikiya Yasmin Husaj ta ce lallai ta ɗamfaru da Ahalulbait (a.s) ne ta hanyar ƙissoshin da ta dinga saurara a wuraren muhadarorin addini.
May 24 2024
Ƙissar Istibsarin Lauyan Jordan (Attorney) Ahmad Husain Ya’aƙub
Ƙissar Istibsarin Lauyan Jordan (Attorney) Ahmad Husain Ya’aƙub
Mujallar Mimbar a fitowarta ta ranar 10 ga watan zulhijja 1421 Hijiriyya, ta wallafa bayanin Ahmad Husain Ya’aƙub a inda yake sanar da yadda ya yi istibsari da kuma karkatarsa zuwa ga Mazahabar Ahalilbaiti (a.s), saƙon Mujallar ya zo kamar haka:
May 22 2024
Yaya Aka Yi Kika Ƙuduri Aniyar Canja Mazahaba? Lallai Ina Ga Labarin Nan Zai Yi Daɗin Ji
Yaya Aka Yi Kika Ƙuduri Aniyar Canja Mazahaba? Lallai Ina Ga Labarin Nan Zai Yi Daɗin Ji
Wannan labari, labari ne mai tsawo sai dai zan faɗe shi a taƙaice, haka ne ni a da ‘yar Ahalissunna ce kuma ‘yar ɗariƙa. Sai dai ƙwaƙwalwata cike take da tambayoyi. Ina son in san mene ne bambanci tsakanin Sunna da Shi’a. To kuma a saboda haka ne wata rana sai na tafi Zariya, garin da Shek Zakzaki yake rayuwa, a can na ci karo da wasu mata uku sanye da baƙin hijabi, abin sai ya ƙayatar da ni, don kafin wannan lokacin ban taɓa ganin mace da kammalalliyar shiga irin haka ba. Shin me wannan yake nufi, kuma mece ce ma’anar mace ta rufe ilahirin jikinta tun daga sama har ƙasa da baƙin hijabi? Na tambayi goggota. Sai ta ce: Mai ya sa kike tambaya? Ki fita harkarsu ba ruwanki da su! Amma ni wannan maganar ta goggota sai ta sa na ƙara nacewa a kan sai na san dalili.
May 19 2024
Farfesan Jamus wanda ya zama Shi’a
Farfesa Roderick Agurman
Mashahurin Farfesan Jamus ‘Roderick Agurman’ Ya Shi’ance
Kasantuwar yana son Musulunta, sau uku yana karance Ƙur’ani, Farfesa Roderick Agurman mutum ne mashahuri a nahiyar Turai, mamallakin babban ɗakin gwaje-gwaje na micro Biology a ƙasar Swiss, kuma shi malami ne na tattalin arziki.
May 18 2024
Na Yi Izgilanci Ga Husain (a.s); Sai Kuwa Allah Ya Kafe Ni Tsugune Waje Guda
Na Yi Izgilanci Ga Husain; Sai Allah Ya Kafe Ni Tsugune Waje Guda
Wasiƙar ɗaya daga cikin ‘yan uwan da suka yi Istibsari:
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. ‘Yan uwana ina son in ba ku wani labari game da ni kaina da kuma yadda Allah ya yi mani uƙuba yayin da na yi wa Imam Husain (a.s) izgilanci… Na kasance riƙaƙƙen Bawahabiye. Ba na son Shi’a ko kaɗan, ina ma kafirta su ne kai tsaye, sam-sam ba na masu fatan alheri, kullum ina yi masu tahadidi, sannan ina zaginsu, ina ci masu mutunci… Ana nan sai kawai wata rana cikin ranakun Ashura, ina zaune a gaban talabijin ina kallon tashar ‘yan Shi’a suna ta kuka suna dukan ƙirjinsu domin juyayi (na kisan gillar) da aka yi wa jikan Manzon Allah (s)…
May 18 2024
Ƙissar Shi’antar Sayyid Husain Dargami Ɗaya Daga Cikin Manya-Manyan Malaman Azhar
Ƙissar Shi’antar Sayyid Husain Dargami Ɗaya Daga Cikin Manya-Manyan Malaman Azhar
Shi ne babban malami Husain Dargami wanda Jami’ar Azhar ta yaye kuma ya fita da sakamako mai kyau, bayan ya kammala Jami’ar sai ya fara bincike a kan asali, tsatso da nasabarsa; to bayan wannan bincike mai tsawo, sai kawai ya karkato zuwa ga Mazahabar Ahalulbaiti (a.s) a hannun marigayi Ayatullahil Uzma Sayyid Abul Ƙasim Khu’i, shugaban ‘yan Shi’a na wancan lokacin. Kuma ya yi karatu a Jami’ar Addini Najaf tsawon wani lokaci, sannan ya koma Alƙahira, yayin da ya zama wakilin Marja’iyyar Shi’a a can.
May 12 2024
Shek Khalil Hashim Ɗaya Daga Cikin Labanawa Masu Tahƙiƙi
Shek Khalil Hashim Ɗaya Daga Cikin Labanawa Masu Tahƙiƙi
Ni mazaunin wata unguwa ne a Labanon unguwar da mafi yawan mazaunanta suna da zaƙewa a cikin lamarin Sunna, sai dai ba wai kawai ba su da masaniya a kan Shi’anci ba ne, a’a hatta Sunnanci nasu ma ba wani ilimin kirki suke da shi a kansa ba…
Tattaunawa da su ba riba, kawai sai dai ma
May 8 2024
Luca Gaetani Lovatelli Ya Shiga Musulunci Bisa Mazahabar Shi’a
Ya Shiga Musulunci Bisa Mazahabar Shi’a
Luca Gaetani Lovatelli ya fito daga cikin babban gida a Italiya, an haife shi a shekarar 1955, a matsayinsa na mai ɗaukar hoto (camera man) a gidan tv na ƙasa, Luca ya yi tafiye-tafiye zuwa Bosnia da kuma Yammacin Asiya.
Bayan nan ya samu yin tafiya zuwa Afganistan, shi da wani abokin ƙuruciyarsa Edoardo Agnelli, domin aikin tattara bayanai na tarihin ƙasar Afganistan ɗin, wato (documentary).
Luca ya fahimci wani abu a kan addinin Musulunci daga wajen abokinsa Edoardo.
A shekarar 1988, Luka ya yi tafiya zuwa Iran tare da Edoardo, to bayan wata doguwar tattaunawa da suka yi da Muhammad Hasan Qadiri-Abyane; sai ya zama ɗan Shi’a.
A ranar 2 ga April 2007, an tsinci gawarsa, amma an ga alamun bugu a jikin gawar tasa, duk da wannan, amma sai kotu ta kulle shari’ar ƙarar da aka shigar ta mutuwarsa, aka masa hukunci da cewa wai kisan kai ya yi kamar yadda aka yi wa (abokinsa) Edoardo shi ma.
By english • Autobiographies of converts(of those converted to Shiaism) • 0 • Tags: Converted ot shia, Edoardo Agnelli, Islam, Luca Gaetani Lovatelli, Mostabserin, Shia
Wallafe-wallafen Mustabsirin
Jan 22 2024
A Albarkacin Hasken (Sayyida) Fatima Na Shiriya
A Albarkacin Hasken (Sayyida) Fatima Na Shiriya
Sunan Littafi: A Albarkacin Hasken (Sayyida) Fatima Na Shiriya
Marubuci: Abulmun’im Hasan Sudani
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai; wannan littafi labari ne mai ratsa zuciya na wani masanin shari’a mutumin Sudan game da yadda ya fahimci mazahabin Ja’afariyya (Shi’a Imamiyya)
Feb 3 2024
LITTAFIN: ALBID’ATU WAL IBTIDA’U
ALBID’ATU WAL IBTIDA’U; Ta’alifin Abdulhamid Al-Jaf.
Silsilatul Kitabi Wassunnati (Halƙa Ta Uku).
Halƙa Ta Uku
Wannan Littafi A Halƙarsa Ta Uku Ya Ƙunshi: Sujjada A Kan Turba Da Bayyana Bisimillah (A Cikin Salla) Da Haɗa Salloli Da Shafa a Kan Ƙafa Da Ɗora Hannu A Kafaɗa Da Sakin Hannu Da Taƙiyya Da Mutu’a.
Dukkan waɗannan bahasosin an yi su a cikin wannan littafin tare da kawo hujjoji da dalilai daga Alƙur’ani da Sunna Sharifiyya.
Littafin an rubuta shi da harshen Larabci, muna ƙoƙarin tarjama shi zuwa harshen Hausa ba da jimawa ba insha Allah.
Mar 13 2024
Hankali a Rayuwar Dan’adam / Dr. Ammar Al-Makki
A cikin wannan shiri mutum zai karu da bayani game da wasu ka’idodi na bahasin Hankali. Shi ko hankali kamar yadda muka sani a gaskiyar magana shi ne mutum saboda ba a komai da marar hankali a rayuwar nan, kai ba a ma lissafa marar shi a matsayin mutum. To kuma a lokaci guda ma’abocin hankalin shi ma yana bukatar ya saita hankalin nasa bisa ka’idodi….Wanda a nan za a ji wasu daga ciki.
Mar 14 2024
ZAGIN SAHABBAI BA MUSULUNCI BA NE1 / MALAM BELLO DANKOLI
Har kullum bayanan da Shi’a suke yi shi ne: Tabbas ba sa zagin sahabbai, domin zagi a Musulunci haramun ne, aya ta fada mana cewa: Kada ku zagi wadanda suke kiran wanin Allah…. Wato Mushirikai da kafirai. To idan zagin su Allah ya hana, ina ga zagin Musulmai kuma Musulman ma sahabbai wadanda suka taimaki Annabi wajen isar da wannan sako na Musulunci.
To amma inda gizon ke saka shi ne: Shi’a suna karanta abubuwan da suka faru a zamanin sahabbai na rigingimu da sakin hanyar da wasu suka yi da kin bin umarnin Annabi na wasici da ya yi masu a Gadir Khum da dai sauran matsaloli. Sai dai mu sani ba fa wai dukkan sahabbai ne suka aikata ba a’a tarihi bai bar mu a duhu ba, ya zayyano mana wadanda suka yi din. Mutum ya je ya bincika zai gani. Fadin hakan kuma ba zagi ba ne sam.
Tarihin Rayuwar Mustabsirin
Jun 18 2024
Mu San: Shibuli Sharif Ibrahim a Takaice
Takaitaccen Tarihin Sayyid Sharif
Shibuli Sharif Ibrahim
🧿 Haihuwa: An haife shi a unguwar Warure da ke cikin birnin Kano.
🧿 Fadi-tashi na ilimi: Ya yi karatun Alkurani a gidansu a gaban baffansa Sidi Yaro da malam Musa Aminu da malam Awwalu, sannan ya tafi tsangayar malam Tijjani.
Haka kuma ya yi karatun ilimi a zaurukan malamai da dama.
💠 Wasu daga cikin malamansa:
1. Malam Murtala Yankatifa.
2. Malam Yahya ‘Yanhaya.
3. Shekh Harazimi Mai Ashafa.
4. Shekh Yahya ‘Yandoya.
5. Malam Buda Rjiyar lemo.
🏮Bayan fahimtar makarantar Ahlulbait (a.s), ya halarci daurori a Iran da Iraki.
📿 Babban abin da ya sa a gaba yanzu shi ne hidimta wa mumbarin imam Hussaini (a.s).
📖 Shekarar da ya fara rubutu: 2009.
📚 Adadin littattafansa: 10.
📚 Sunayen littattafansa:
1. Mahadi Hujjar Allahu.
2. Jagoran Maziyarci.
3. Ranar Ashura.
4. Hukuncin Kafa A Alwala.
5. Laduban Zaman Makokin Ashura.
6. زاد الزائر إلى كعبة الأحرار.
7. زاد الطالب من أحاديث الأداب* *8.قبة الخضراء من أحاديث الزهراء.
9. وسائل الجاني ومسائل الفاني.
10. أربعون حديث في التوحيد.
🧿 Email: sharifshibuli085@gmail.com
Jun 4 2024
Daga Ɗariƙar Ƙadiriyya Zuwa Shi’anci
Daga Ɗariƙar Ƙadiriyya Zuwa Shi’anci
Ganawa da tattaunawa ta ƙud da ƙud da mustabsiri ahalin gundumar Kurdistan ɗin Iraƙi, malam Isa Barzanji, kuma ya ba da labarin yadda ya yi istibsari abin gwanin ban sha’awa kamar haka:
Tarihin Rayuwa:
Ni hadimin Abu Abdillah (a.s) ne a jahar Sulaimaniyya babban birnin al’adun gundumar Kurdistan ta Iraƙi, kuma shugaban al’amuran addinin Musulunci da alaƙoƙi a Husainiyyar Imam Hakim a garin Sulaimaniyya. Sai dai abin damuwa wannan shi kaɗai ne ginin Husainiyya a duk faɗin gundumar Kurdistan.
Ni Shi’a ne kuma mustabsir. Amma a da ni ɗan mazahabar shafi’iyya ne a bisa tafarkin ɗariƙar Ƙadiriyya, cikin godiyar Allah yanzu kam ni ina a kan mazahabar Isna Ashariyya kuma ɗariƙar Ahalulbait (a.s).
Jun 2 2024
A Haramin Imam Rida (a.s) Na Yi Alƙawarin Zama Shi’a
Malam Amin Ƙasim Abadi
A Haramin Imam Rida (a.s) Na Yi Alƙawarin Zama Shi’a
Labarin wani matashi mutumin Binalud mai suna malam Amin Ƙasim Abadi, wanda yanayin yadda ya sami waraka albarkacin karamar Imam Rida (a.s) ya zama abu mai matuƙar ƙayatarwa da buƙatar zurfin tunani.
Ga Yadda Ya Ba Da Ƙissar Da Kansa Kamar Haka:
Ni haifaffen shekara ta 1366sh (Hijira Shamsiyya) kuma a yanzu haka ina zaune a Mashhad. Ina ɗan shekara shida na rasa mahaifina, bayan nan sai muka koma gidansu mahaifiyarmu a (ƙauyen) Binalud. Mahaifiyata takan yi saƙar darduma kuma a nan ne take samun ‘yan kuɗin da take mana hidimar yau da gobe, wanda wannan abin shi ne ya haifar mata da gushewar ganinta har ta makance. Ɗan uwana kuma a saboda maraicin rashin uba ya kama shaye-shayen ƙwayoyi. Duk da cewa danginmu da ni kaina duk ‘yan Ahalissunna ne amma sam ba su damu da halin ƙuncin da muka samu kanmu a ciki ba.
May 31 2024
Hasken Shiriyar Ɗalibi, Ya Zama Sanadin Shi’ancewar Malami
Hasken Shiriyar Ɗalibi, Ya Zama Sanadin Shi’ancewar Malami
‘Yar dubiya ‘yar kaɗan a cikin tarihin rayuwar wani malami ɗan Sunna wanda ya zama Shi’a a Pakistan, shek Hafiz Ali Muhammad Fatahuddin Hanafi’.
Tasowarsa Da Karatunsa
An haifi Ali Muhammad Fatahuddin
Bugawar Cibiya
Jan 24 2024
Bugawa Da Yaɗa Mujalladi Na Farko Na Littafin (Mausu’ar) Mustabsirin
Littafin (Mausu’ar) Mustabsirin
Cikin luɗufi na Ubangiji da inaya ta Ahlul Bait Ma’asumai (a.s) tare da tsayuwar-daka da himmar kwamitin ilimi na Cibiyar Mustabsirin wannan littafin (Mau’su’ar) Mustabsirin an kammala buga shi da yaɗa shi.
An fara yaɗa mujalladi na farko na littafin (Mau’su’ar) Mustabsirin daidai da ranakun tunawa da Shahadar Sayyida Fatima Azzahra (s).
Jan 22 2024
Littafin: Aƙidar Tauhidi a Makarantar Ahlulbait (a.s)
Littafi Mai Daraja Da Aka Rubuta Game Da (Aƙidar Tauhidi a Makarantar Ahlulbait (a.s))
A kwanakin Idin Gadir mai girma da albarka, Cibiyar Mustabsirin ta himmantu da buga tare da yaɗa littafi mai ɗimbin daraja mai suna: (Aƙidar Tauhidi a Makarantar Ahlulbait (a.s)) wato Aƙidar Tauhidi a bisa koyarwar makaranta ta tunani da fikira ta Ahlulbait (a.s), mawallafin littafin shi ne Dakta Ahmad Rasim Al-Nafis mustabsir kuma mutumin Masar.
Wane ne Ahmad Rasim Al-Nafis
– Sayyid Ahmad Rasim Al-Nafis Ma’abocin Himma a Musulunci (Islamic Activist).
– Dan Shi’a Imamiyya.
Dakin Karatu
Mar 21 2024
Fadlul Shi’ati Alal Ummati Fi Hifzil Ƙur’ani Wal-inayati Bihi – Ustaz Marwan Kalifat
Cikin godiya ga Allah fitowar wannan littafi ta kammalu:
Fadlul Shi’ati Alal Ummati Fi Hifzil Ƙur’ani Wal-inayati Bihi
(فضل الشيعة على الأمة في حفظ القرآن والعناية به)
Falalar Shi’a a kan (Sauran) Al’umma
Falalar Shi’a a kan Al’umma a wajen kiyaye Ƙur’ani da kulawa da shi da Shakkala shi da yi masa nuƙuɗa-nuƙuɗa da Tafsirinsa.
Wallafar: Ustaz Marwan Kalifat
Wani yanki na muƙaddimar littafin: Wahabiyawa da waɗanda suka tasirantu da koyarwarsu suna aibata Shi’a kuma suna yawan tuhumar su a kan su kawo ingantaccen sanadi na Ƙur’ani. Yana da ban mamaki lamarin tuhumar nan tasu! Domin wanda gidansa ya kasance na gilas ne, ba zai jefi gidajen mutane da dutsi ba, kamar yadda yake a karin-magana. A saboda haka shin su ɗin sun mallaki ingantaccen sanadin, ballantana a yi maganar tawaturinsa ga ƙira’ar Hafs wacce mafi agalabin Musulmai suke karantawa a yau?!
Mar 13 2024
Husain (a.s): Tsakanin Haihuwa da Shahada Cikin Ruwayar Zahabi da Haisami
Sunan Littafi: Husain (a.s) A Tsakanin Haihuwa Da Shahada Cikin Ruwayar Zahabi Da Haisami.
Sunan Littafi na Asali: (Al-Husain Alaihil Salam Bainal Wiladati Wal Shahadati Fi Ruwayatil Zahabi Wal Haisami).
Mawallafin Littafi: Shek Nazar Aali Sanbul Al-Ƙaɗifi.
A Dunƙule Littafin ya ƙunshi:
Feb 18 2024
Wahada a tsakanin Muwahhidin
Kira zuwa ga Wahada!
Kira ne na Alƙur’ani wanda ayoyi sukutum Allah (swt) ya saukar domin haɗin kai a tsakanin muwahhidin wato masu addinin saukakke daga Allah (swt) wanda ya ƙunshi dukkan abubuwan da ake buƙata na haɗin kai (saboda yadda haɗin kan yake da matuƙar muhimmanci da kuma fa’idar da ke cikin yin hakan).
Feb 5 2024
Littafi: Ayatul Taɗhir
Littafi: Ayatul Taɗhir
Mawallafi: Muhammad Mahadi Asifi
Bugawar: Majma’ul Alami Li Ahlil Bait (a.s)
Sura: Ahzab; Aya ta 33: Bismillahir rahmanir rahim: Innama yuridullahu li yuzhiba ankumur rijsa Ahlal Baiti wa yuɗahhirakum Taɗhira.
Mawallafin littafin ya yi ƙoƙari sosai wajen kawo hujjoji daga Sunna da Shi’a game da fayyace cewa shin wai su wa ake nufi a wannan aya mai girma, haka nan ya kawo lawazim ɗin da ke tattare da ayar kama daga batun Isma da Tsarki da Tsarkaka daga dukkan datti ko saɓo da sauransu da kuma hukunce-hukunce na shari’a da aka iya fitarwa daga ciki.
Feb 3 2024
LITTAFIN: IMAMA DA WILAYA A ALƘUR’ANI
Littafi ne da wasu adadi na malamai suka wallafa a kan Imamancin Ahlul Baiti (a.s) a Alƙur’ani mai girma da hadisai sharifai.
A cikin littafin sun kawo dalilai masu tarin yawa daga Alƙur’ani mai girma da Sunna Sharifiya domin tabbatar da jagorancin Ahlul Baiti (a.s) cewa lallai Manzon Allah (s.a.w) ya naɗa wa al’ummar Musulmi waɗanda za su jagorance su a bayansa kuma ya shelanta masu cewa madamar suka yi ri ƙo da su to ba za su taɓa ɓata ba a bayansa har sai sun same shi a tafkin Kausara.
Daga cikin ruwayoyin akwai inda Manzon Allah (s.a.w) yake cewa: “Lallai ni mai bari a cikinku ne Nauyaya guda biyu (Saƙalain); (ko Abubuwa masu Daraja da Ƙima guda biyu; (Siƙlain): madamar kuka yi riƙo da su to ba za ku taɓa ɓata ba har abada, kuma lallai su ba za su taɓa rabuwa ba har sai sun iske ni a tabki (tabkin Kausara)).
Jan 5 2024
TAUHIDIN MUFADDAL
KASHI NA FARKO
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI
TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA ANNABI MUHAMMADU DA IYALAN GIDANSA TSARKAKA
GABATARWAR MAI YADAWA
Imaman Ahlul Baiti (a.s) sun kasance suna ƙosar da al’ummah da iliminsu, suna amsa tambayoyin masu tambaya, suna bude ƙofofin sani ga masu nema.
Haƙiƙa Imam Jafar dan Muhammad Al-Sadiƙ (as) yana daga cikin wannan bishiyar mai tsawo da faɗi, kuma bishiyar da tushenta ya tabbata kuma ya kafu a cikin ƙasa, ya yi amfani da wata dama ta raunin daular Umaiyawa, da kuma lokacin da Abbasiyawa suke ƙoƙarin assasa daularsu, saboda haka sai ya assasa babbar makarantarsa ta tunani (hankali), sai daliban ilimi da haƙiƙa suka tuttuɗo gare shi suna kwasar ilimi daga tushensa, More
Apr 6 2024
Shiga Cikin Ƙunci Da Tsananin Rayuwa Ya Zama Sanadin Shiriyata
Shiga Cikin Ƙunci Da Tsananin Rayuwa Ya Zama Sanadin Shiriyata
Bayan bincike mai zurfi da nacewa kan yin addu’oi, na tsinci kaina ina mai miƙa wilayata ga Imam Ali (a.s) a matsayinsa na hasken Musulunci, kuma magajin Manzon Musulunci na haƙiƙa, wanda Allah ne da kansa ya zaɓe shi, ya wajabta mana ƙaunarsa da yin biyayya gare shi.
Ni haifaffiyar ƙasar Czech ce (Jamhuriyyar Czech:) a nan aka haife ni kuma a cocin Katolika aka yi bikin raɗa mini suna domin neman tabarruki, duk da cewa iyayena ba wasu masu kula da addini ba ne can sosai ba, amma dai mun yi imani da Allah sai dai ba ma yin bautar sam-sam. Lokacin da na kai shekara 14 a duniya a lokacin ne na rasa mahaifiyata. Ina ‘yar shekara 18 kuma na yi aure, yanzu haka ina da ɗa a auren da na yi. Amma kasantuwar ƙarancin shekaru, zamantakewar wannan aure sam ba ta yi daɗi ba, zaman aure sam babu fahimtar juna a tsakani.
More
By hs • Kundin Tattara Bayanan Mustabsirin (Encyclopedia) 0