Wahada a tsakanin Muwahhidin

Kira zuwa ga Wahada! Kira ne na Alƙur’ani wanda ayoyi sukutum Allah (swt) ya saukar domin haɗin kai a tsakanin muwahhidin wato masu addinin saukakke daga Allah (swt) wanda ya ƙunshi dukkan abubuwan da ake buƙata na haɗin kai (saboda yadda haɗin kan yake da matuƙar muhimmanci da kuma fa’idar da ke cikin yin hakan).