Bugawa Da Yaɗa Mujalladi Na Farko Na Littafin (Mausu’ar) Mustabsirin

Littafin (Mausu’ar) Mustabsirin Cikin luɗufi na Ubangiji da inaya ta Ahlul Bait Ma’asumai (a.s) tare da tsayuwar-daka da himmar kwamitin ilimi na Cibiyar Mustabsirin wannan littafin (Mau’su’ar) Mustabsirin an kammala buga shi da yaɗa shi. An fara yaɗa mujalladi na farko na littafin (Mau’su’ar) Mustabsirin daidai da ranakun tunawa da Shahadar Sayyida Fatima Azzahra (s).