‘Yan Ƙasar Jamus Waɗanda suka yi Istibsari a Kufa
‘Yan Ƙasar Jamus Masu Istibsari a Kufa Wani rukunin ‘yan ƙasar Jamus waɗanda suka yi istibsari sun sami ziyartar Masallacin Kufa da kuma Hubbaren Sayyiduna Muslim bn Aƙil (a.s)
‘Yan Ƙasar Jamus Masu Istibsari a Kufa Wani rukunin ‘yan ƙasar Jamus waɗanda suka yi istibsari sun sami ziyartar Masallacin Kufa da kuma Hubbaren Sayyiduna Muslim bn Aƙil (a.s)
HAIHUWAR IMAM RIDA (A.S) ZIYARAR KABARIN IMAM ALI AR-RIDA(AS) DA TAWASSULI DA SHI; YA NA SA ALLAH YA KARBI ADDU’A, YA BIYA DA BUKATA. – INJI IBN HIBBAN (BABBAN MALAMIN AHLUS-SUNNAH). Ibn Hibban: Babban malamin Ahlus-sunnah ne. Darul-Dutni, Al-Hakim (marubucin Al-Mustadrak)… su na daga cikin dalibansa. Littafin sa As-Siqat (الثقات); sika ne kuma marja’i a […]
Sayyida Lima Hamade ‘Marubuciya Daga Dameshƙ’ Ɗaya daga cikin kyawawan littafanta shi ne: ‘Akhiran Ashraƙatil Ruh’ (أخيراً أشرقت الروح) wanda yake nuna zurfin imanin wannan matashiya a cikin Shi’anci da kuma tattaunawarta ta musamman… Ko shakka babu ina mai tabbatar da cewa lallai Allah ya shirye ni zuwa ga karɓar sahihiyar koyarwar addini bisa tafarkin […]
Ranar 1 ga watan Zulƙa’ada, rana ce ta farin ciki da murna ga muminai, saboda a cikinta ne aka haifi Karima, Jalila, Sayyida Fatima Ma’asuma ‘yar Imam Musal Kazeem (a.s). Wannan baiwar Allah mai girma, wacce a cikin ziyararta ake mata kirari da cewa: “’Yar waliyiyar Allah, ‘yar uwar waliyin Allah kuma goggon Waliyin […]
Ziyarar Shugaban Hauzozin Ilimi Cibiyar Duniya ta Mustabsirin Shugaban Hauzozin Ilimi a Iran Ayatullah A’arafi Shugaban Hauzozin Ilimi a Iran Ayatullah A’arafi ya kawo ziyara ta musamman zuwa Mu’assasar Imam Hadi (a.s) da ke Qum; inda shugabannin wannan Mu’assasa suka yi masa tarba ta musamman, to a cikin wannan ziyara tasa ya kuma ziyarci sashen […]
JUYAYIN SHAHADAR IMAM JAFAR AS-SADIƘ (a.s) ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD WA AALI MUHAMMAD A watan Shawwal ranar 25 gare shi a shekara ta 148H, Imam Jafar As-Sadiƙ (a.s) ya yi Shahada. Imam Jafar Assadiƙ (a.s) shi ne Imami na shida (6) daga cikin Limaman shiriya na gidan Annabta, wadanda Manzon Allah (s) ya yi […]
Ladar Sanar da Al’umma Makarantar Ahalulbait a Mahangar Mirza Shirazi Ƙoƙari da ƙwazon shekaru 15 sun yi sanadin canja ƙauyen ‘yan Sunna zuwa Shi’a Ayatullah Wahid Khurasani (Allah ya ƙara tsawon kwana): A zamanin Mirza Shirazi wani ɗalibi ya zo ƙofar gidansa yana sanye da tsofaffin kaya ya ce: “Ina son ganin Mirza… Mutane […]
A ranar Juma’a 18 ga watan Ramadan 1445 bayan Hijira dalibai mazauna unguwar Shaharake Mahadiyye wadanda suka hada daga ‘yan kasashe daban-daban na Afrika da kuma ‘yan kasashe irin su Pakistan da Indiya da Indunisiya da Siriya da sauransu suka gudanar da munasabar raya daren lailatul Kadari domin neman tabarruki da neman kusanci zuwa ga […]
DAREN DA AKA SARI AMIRUL MUMINA ALI (a.s) 19 Ramadan shekara ta 40 bayan Hijira Tarihin faruwar wannan abin yana da tsawo, to amma bisa la’akari da lokaci da kuma saƙon da ake son a isar a wannan taƙaitaccen rubutun a kuma dare irin wannan na 19 ga watan Ramadan, sai mu ce: Bayan yarjejeniyar […]
Ta’aziyyar Wafatin Allamatul Kaurani (r.a)
Waɗanda suke idan wata masifa ta same su, sai su ce: Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’una. Cike da jimami da baƙin ciki muka samu labarin wafatin babban malami ma’abocin tahaƙiƙi da bahasi, marigayi abin nema wa gafara (a wajen Allah); Allama Shek Ali Kaurani Al’amuli (r.a). Muna miƙa ta’aziyyarmu ga ɗaukacin Musulmi, musamman dai […]